<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>97</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ba wani suna na ke so in ji, in riƙa ji.
 Yesu, sunanka dā da yau har ahada ya fi.

[V2]
 2) Ba wani sunan da zai sa mu zo mu riƙa zuwa,
 Ciki mu nemi mafaka, ciki mu yi addu'a.

[V3]
 3) Yesu, sunanka ya kan ba Mai Binka iko na
 Yin yaƙi har da nasara, ya sami hutu can.

[V4]
 4) Sunanka ya kan tsorata Shaiɗan, maƙiyinmu.
 Ransa zai ƃāci in ya ga ƙaunarka cikinmu.

[V5]
 5) Ba mu da ikon yabonka, ya wuce faɗinmu,
 Sai ran da za mu gan ka can, Yesu Masoyinmu.</lyrics>
<title>Ba Wani Suna Na Ke So In Ji, In Riƙa Ji LW97</title>
</song>